An kamo hanyar Magance labarun bogi a Arewa

0 125

Cibiyar Dimukuradiyya da Cigaba a Nahiyar Afrika (CDD) ta kaddamar da taron gangamin lalubo yaki da labarun karya da na bogi marasa tushe da makama a Arewacin Nijeriya a safiyar yau Litinin.

A karon farko dai cibiyar ta shirya gangamin ne ta hanyar intanet (virtual), tare da hadin kan kungiyoyi kamar Bridge4Innovation, Curator 100 Women in Tech Nigeria and Hackathon International.

Idayat Hassan

A baya-bayan nan samun labarai masara tushe a kafafen yada labarai sun yawaita musamman a kafafen sadarwa na zamani a Nijeriya, mafi yawancin lokuta irin wadannan labaru sun danganci gwamnati, siyasa, annoba, da kuma tsaro.

Irin wadannan labarai dai baya ga rashin tushe da madafa da suke da shi, har ma suna iya haddasa husuma da rikici wanda ka iya janyo asarar dukiya ko rayuka.

Karuwar samun labarun bogi da kuma yawaitar yan Nijeriya masu amfani da kafafen sadarwa na daga cikin dalilin da ya sanya CDD da takwarorinta suka ga dacewar shirya gangamin don a lalubu sahihun hanyoyin magance karuwar labarun bogi.

A cewar Daraktan CDD Idayat Hassan, gangamin dai zai mayar da hankali ne wajen fito da hanyoyin magance;

  1. Labarun karya da na bogi marasa tushe a fannin tsaro
  2. Labarun karya da na bogi marasa tushe a fannin Annoba
  3. Labarun karya da na bogi marasa tushe a fannin zabe
  4. Labarun karya da na bogi marasa tushe a fannin tafiyar da gwamnati

Akwai kyauta mai kwabi da aka tanadar ga duk wadanda suka fito da gamsassun hanyoyin yaki da labarun karyar a karshen gangamin.

Yau ce ranar farko a taron da za a shafe ranaku 3 ana gudanar da shi ta hanoyiyn sadarwar zamani (intanet)

Leave a Reply

%d bloggers like this: