APC Ta Lashe Zaɓen Dan Majalisa Mai Wakiltar Gumel, Gagarawa, Sule-Tankarkar Da Maigatari

0 218

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana Nazifi Sani na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Gumel, Gagarawa, Suletankarkar, Maigatari a jihar Jigawa.
Da yake sanar da sakamakon zaben jiya a Gumel, jami’in sanar da sakamakon zaben yace Nazifi Sani ya samu kuri’u dubu 49 da 893 inda ya kayar da abokin karawarsa, Ahmed Habu Gumel, na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u dubu 46 da 537.
A wani labarin makamancin wannan, hukumar ta INEC ta ayyana Muhammad Ado Zoto na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar dokokin jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Yankwashi.
Da yake sanar da sakamakon zaben jiya a Karkarna, helkwatar karamar hukumar Yankwashi, jami’in bayyana sakamakon zaben yace Mohammad Ado Zoto na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 9 da 479 inda ya kayar da abokin takararsa, Abdullahi Musa Karkarna na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u dubu 5 da 606.

Leave a Reply

%d bloggers like this: