INEC Ta Bayyana Ibarahim Kabiru Na PDP A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Kujerar Wakilcin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu.

0 111

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Ibrahim Kabiru a matsayin wanda ya lashe zaben cike gibin majalisar dokokin jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Birnin Kudu.
Jami’in kula da zaben Farfesa Usman Haruna na Jami’ar Tarayya Dutse ya bayyana Ibrahim Kabiru a matsayin wanda ya lashe zaben jiya a Birnin Kudu.
Ya ce Ibrahim Kabiru ya samu kuri’u dubu 36 da 50 inda ya doke babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar APC, Muhammad Surajo wanda ya samu kuri’u dubu 34 da 545.
A halin da ake ciki, hukumar zabe ta INEC ta bayyana Ishaq Tasiu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar dokokin jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Dutse.
Jami’in kula da zaben yace Ishaq Tasiu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 31 da 311 inda ya kayar da Adamu Alhaji Musa Zai na PDP wanda ya samu kuri’u dubu 28 da 656.

Leave a Reply

%d bloggers like this: