Bangarorin Sojojin Kasar Sudan Sun Amince Da Sabunta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

0 75

Bangarorin da ke hamayya da juna na sojojin kasar Sudan sun amince da sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku.

Tsawaita wa’adin da wasu sa’o’i 72 ya biyo bayan gagarumin kokarin diflomasiyya da kasashe makwabta, da Amurka da Birtaniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka yi.

Sai dai ana ci gaba da samun rahoton kazamin fada a babban birnin kasar Khartoum.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da ta gabata ta bai wa dubban mutane damar kokarin guduwa domin tsira, yayin da kasashe da dama suka yi kokarin kwashe ‘yan kasarsu.

An shafe kusan makonni biyu ana gwabza fada tsakanin sojoji da wata kungiyar sa-kai da ke gaba da juna, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Da sanyin safiyar jiya ne sojojin Sudan din suka amince da tsawaita wa’adin tsagaita wutar, kuma dakarun kungiyar RSF suma sun bi sahu bayan wasu sa’o’i. Sudan ta Kudu ta yi tayin karbar bakuncin tattaunawar zaman lafiya, kuma rundunar sojin kasar ta amince da tura wakilai zuwa tattaunawar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: