Wata Mata Ta Cinnawa Kanta Wuta Bayan Ta Gano Cewa Saurayinta Yana Yaudararta

0 74

Wata mata mai shekaru 35 mai suna Maryam Aminu ta bankawa kanta wuta bayan ta zargi saurayinta da yaudara a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta farin kaya civil defense a jihar, Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na dare a unguwar Gindin Dinya da ke Dutse.

Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa matar ta yi amfani da fetur ne ta cinna wa kanta wuta.

Ya kara da cewa wasu mutanen unguwar ne suka kashe wutar tare da ceto ran matar.

Wani ganau ya ce matar ta fusata ne lokacin da ta samu labarin cewa saurayin nata ya je wajen wata mata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: