Sama Da Daliban Najeriya 500 Sun Makale Akan Iyakar Masar Da Sudan

0 81

Sama da daliban Najeriya 500 da aka kwashe daga Khartoum babban birnin kasar Sudan da yaki ya daidaita zuwa Masar sun makale a kan iyakokin kasashen biyu.

Sama da 100 daga cikinsu sun makale a wani kauye mai suna Wadi Halfa, kasa da kilomita 100 daga Masar bayan an kubutar da su wajen amfani da motocin Bas.

An gano cewa jakadan Najeriya a Masar da wasu jami’ai suna bakin iyaka suna jiran karbar daliban, amma sun kasa wucewa a daren jiya.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa daliban da ke Wadi Halfa an jefar da su ne a wani fili kuma suna kwana a bene.

A cikin wata sanarwa da ta aikewa manema labarai, wata majiya mai masaniyar lamarin ta ce gazawar masu ruwa da tsaki wajen yin aiki tare ne ya janyo gararanbar yan nigeriyan. Kawo yanzu dai angano cewa ofishin jakadancin Najeriya da ke Sudan ba’a basu kudaden da za su biya kudin motocin bas din da sukayi jigilar su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: