JAMB Ta Nuna Damuwa Kan Kutsen Da Mahukuntan Wasu Fitattun Makarantu Suka Yi

0 76

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta nuna damuwa kan abin da ta kira kutsen da mahukuntan wasu fitattun makarantu suka yi, wajen tallafawa dalibansu.

Hukumar ta ce ya kamata mahukuntan makaranta su gane cewa, hukumar Jamb ba Hukumar Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) da Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) ba ce.

Mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin, a wata sanarwa da ya fitar jiya ya ce, makarantu ba su da wata rawar da za su taka wajen shiga lamarin hukumar JAMB.

Ya ce hukumar ta sha gargadin mahukuntan manyan makarantu da su daina kutsawa cikin ayyukan hukumar domin kada su yi illa ga makomar ‘dalibai Kawo yanzu dai kimanin dalibai 60,000 ne aka tabbatar da cewa an tallafa musu wajen zana jarrabawa cikin dalibai miliyan 1.6 da sukayi rijista.

Leave a Reply

%d bloggers like this: