Bayan Lafawar Korona, Gwamnatin Jigawa Ta Bayar Da Gwangilar Miliyoyin Naira

0 75

Majalisar zartarwar jihar Jigawa ta amince da bayar da kwangiloli wadanda kudinsu ya tasamma Naira biliyan daya da miliyan dari takwas a bangarorin ruwan sha da lafiya.

Tsohon kwamishinan yada labarai, matasa, wassani da al’adu na jiha kuma sabon kwamishinan aikin gona, Alhaji Alhassan Muhammad, ya sanar da haka yayin jawabi ga manema labarai bayan zaman majalisar.

Yace an amince da kashe kudi sama da Naira biliyan daya da miliyan dari domin samar da man dizel da sinadaran tsaftace ruwa da kuma gyaran injinan wuta, na tsawon shekara guda.

Alhassan Muhammad yace majalisar ta kuma amince da kashe kudi sama da Naira miliyan dari da casa’in ta takwas domin cigaban aikin babban asibitin Gantsa ta karamar hukumar Buji, yayin da aka amince da kashe kudi Naira miliyan dari da casa’in da takwas domin makamancin wannan aikin a babban asibiti a Garki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: