Wani tsohon Najadu Dake Yiwa Yara Fyade Ya Shiga Hannu A Katsina

0 79

Wani mutum mai shekaru hamsin da daya a duniya wanda yansanda suka kira da mai yawan aikata fyade, an kama shi a jihar Katsina bisa zargin yiwa wasu yara su biyar fyade.

Mutumin mai suna Jabiru Audu, mazaunin unguwar Tundun Yanlahidda a Katsina, ana zargin ya yiwa yara mata biyar fyade, wadanda shekarunsu suka kama daga hudu zuwa goma sha biyu.

Yansanda sunce Jabiru Audu na zaune a gida daya da yaran tare da iyayensu.

Ana zargin yana aikata aika-aikar duk lokacin da kakar yaran wadanda suke zaune a wajenta, ta bar gida domin zuwa suyar kosai.

An gano cewa iyayen yaran ne suka kai rahoton lamarin ga babban ofishin yansanda na Katsina.

Kakakin rundunar yansandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai, inda ya kara da cewa Jabiru Audu ya amsa laifinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: