Gwamnan Jihar Kebbi Ya Umarci Sakataren Gwamnatin Jihar Ya Shiga Tsakanin Sojoji Da Ma’aikatan KAEDCO

0 81

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi yace ya umarci sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri, da ya shiga tsakani a rashin jituwar da aka samu tsakanin sojoji da ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna, bayan yanke wutar da kamfanin yayi a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, ya shiga rana ta hudu.

Ya sanar da haka jiya yayin da yake jawabi a dakin taro na masaukin shugaban kasa dake Birnin Kebbi.

Gwamnan yace kamfanin na wutar lantarki zai sha wahala wajen biyan bashin da ake binsa, muddin masu amfani da wutar basu biya kudin wuta ba.

Tun a ranar Asabar ne kamfanin na wutar lantarki ya yanke wutar lantarki a Birnin Kebbi gabadaya saboda rashin jituwar da aka samu.

A halin da ake ciki kuma, wani babban soja a barikin Dukku dake Birnin Kebbi, wanda ya nemi a sakaye sunansa, yace sojojin da suka je kamfanin basu bani wani ma’aikacin kamfanin ba.

Ya kara da cewa sojojin sun je ne domin mika korafinsu dangane da yadda karancin wutar ya lalata abubuwan da matayensu ke sayarwa domin samun saukin rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: