NEMA Ta Gargadi Mazauna Jihar Kwara Dangane Da Ambaliyar Ruwan Dake Tunkarowa A Bana

0 78

Ofishin hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA na Minna ya gargadi mazauna jihar Kwara dangane da ambaliyar ruwan dake tunkarowa a bana.

Hukumar ta shawarci hakimai da dagatai da shugabannin addinai, musamman wadanda suke kauyuka, da su fara shirye-shirye domin rage illar ambaliyar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga shugabar ofishin hukumar na Minna, Zainab Suleiman Sa’idu, wacce aka bawa kamfanin dillancin labarai na kasa jiya a Ilorin.

Tace gargadin ya zama tilas biyo bayan rahoton hasashen ambaliyar ruwa na shekara-shekara wanda hukumar kula da ruwa ta kasa ta fitar, da kuma rahoton hasashen yanayi na shekarar 2023 da hukumar kula da yanayi ta kasa ta fitar.

Ta kara da cewa rahotannin biyu sun samu ne bayan binciken kimiyya wanda masana suka yi, wanda ya nuna cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a kasarnan a matakai uku na tsanani da matsakaici da kuma na kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: