A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Jigawa ta musanta rahotannin da suka fito daga hukumar kula da alkaluman lafiya ta kasa da ta sanya jihar a cikin jihohin da suka fi fama da talauci a kasarnan.
Mataimakin gwamnan jihar kuma zababben gwamnan jihar mai jiran gado, Malam Umar Namadi, ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ya karbi rahoton kananan kwamitocin mika mulki.
Umar Namadi ya bayyana cewa gwamnati mai ci a karkashin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ta bullo da tsare-tsare da shirye-shirye da dama domin rage radadin talauci da ake fama da shi a jihar. Ya jaddada kudirin sa na ci gaba da aiwatar da dukkan kyawawan manufofi da tsare-tsare na gwamnatin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar domin ci gaban jihar.