Gwamnatinmu Ba Za Ta Yi Watsi Da Duk Wani Aiki Da Gwamnatin Baya Ta Fara Ba – Danmodi

0 67

Zababben gwamnan jihar Jigawa mai jiran gado, Mallam Umar Namadi, ya yi alkawarin kara tabbatar da nasarorin gwamnatin gwamnan da zai gada Muhammad Badaru Abubakar, bayan an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Mallam Umar Namadi ya bayyana haka ne bayan ya samu rahotanni daga wasu kananan kwamitoci na kwamitin mika mulki a ofishinsa da ke Dutse.

Ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatinsa za ta inganta ayyukan more rayuwa da kuma karfafa tattalin arzikin jihar.

Umar Namadi, wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar mai ci, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi watsi da duk wani aiki da gwamnatin Badaru Abubakar ta fara ba.

Umar Namadi ya amince da cewa akwai yawaitar talauci a jihar. Sai dai ya yabawa kokarin gwamnan mai barin gado inda ya ce an samu ci gaba sosai wajen rage fatara da talauci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: