Biyo bayan sauya sheƙar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC, an sake tayar da muhawara kan rikicin masarautar Kano da tambayar ko hakan zai iya shafar matsayin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.
Sai dai gwamnan ya yi watsi da duk wani ra’ayi na cewa sauyin siyasar zai kai ga cire Sanusi, inda ya jaddada cewa matsayin sarkin na nan daram ba tare da wani sauyi ba.
Tsawon kusan shekaru biyu, masarautar Kano na fama da rikici inda sarakuna biyu, Muhammadu Sanusi na II da Aminu Ado Bayero, ke ikirarin zama Sarkin Kano, kowanne na da fadar da yake aiki da ita tare da goyon bayan bangarorin siyasa daban-daban.
An sake nada Sanusi a watan Mayun 2024 bayan majalisar dokokin jihar Kano ta soke dokar da ta kirkiri masarautu biyar, amma duk da haka Aminu Ado Bayero ya ci gaba da ikirarin sarautar, lamarin da ya kara dagula rikicin.
Zargin yiwuwar sulhu ya kara karfi bayan Kwamishinan Labarai na jihar ya ce gwamnati na daukar matakai na dawo da zaman lafiya, abin da ya sa jama’a ke hasashen ko za a sake sauya lamari a masarautar.
Amma a martaninsa, gwamna ta bakin kakakinsa Sanusi Bature ya ce babu wani shiri ko yarjejeniya da za ta kai ga cire Sanusi, yana mai cewa masarautar ba ta cikin duk wata yarjejeniyar siyasa.
A halin da ake ciki, shari’ar da ke gaban Kotun Koli da kuma ra’ayoyi mabambanta daga mazauna Kano na nuna cewa rikicin masarautar na nan daram, yayin da jama’a ke kira da a bar doka da zaman lafiya su yi nasu aiki.