Gwamnatin Najeriya a yanzu ta yi kaurin suna wajen samar da tsare-tsaren takurawa talaka – Atiku

0 97

Tsoshon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya shiga sahun masu tausayawa ma’aikatan Najeriya, inda ya ce, suna aiki karkashin gwamnatin da tai kaurin suna wajen samar da tsare-tsaren takurawa talaka.

Atiku wanda yai wa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a zabukan 2019 da 2023, ya bayyana hakan ne a sakon da ya turawa ma’aikatan Najeriya a ranar ma’aikata ta bana.

Atiku ya ce, a yayin da suka shiga sahun sauran mutanen duniya wajen murnar ranar ma’aikata, halin da ‘yan Najeriya ke ciki ya matukar tsananta.

Ya kara da cewar karin kudaden da ake samu a abubuwa da dama ga ‘yan kasa ba tare da an magance cin hanci da rashawa da rashin yin daidai a al’amura ba, to kawai ana sa ‘yan Najeriya suna bayar da tallafi ne ga cinhanci da rashin iya gwamnati. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: