Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna ta ce jami’an ta sun kama wani mutum da ake zargi da satar mutane da kuma kubutar da wani wani da aka yi garkuwa da shi Abuja.
Kakakin rundunar ‘Yan sandan Jihar ASP Mansir Hassan shine ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a kaduna.
Yace jami’an sun kubutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Abuja, da kuma kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, da kwato makamai da ababan hawa daga hannunmasu garkuwa da mutanen. Kakakin ‘Yan sandan yace kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar ya yabawa jami’an na ‘Yan sanda bisa kokarin da suke na magance matsalar tsaro a Jihar.