Kamfanin BUA zai rage farashin sumunti zuwa ₦3,500 a Najeriya

0 309

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul-Samad Rabiu, ya ce kamfaninsa zai rage farashin sumunti zuwa naira 3,500 a Najeriya.

Abdul-Samad Rabiu ya bayyana haka ne ga manema labarai a fadar shugaban Najeriya, jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu ranar Juma’a da maraice.

Ya ce ya dauki matakin rage farashin sumuntin ne a wani bangare na mara wa Kudurin gwamnatin tarayya baya wajen daidaita farashin muhimman kayayyaki a kasar

Abdul-Samad Rabiu ya kuma ce kamfaninsa zai kara gina wasu sabbin kamfanonin sarrafa sumunti biyu a karshen shekara ko farkon shekara mai zuwa.

Ya ce kamfanonin wadanda shugaban kasar zai kaddamar idan sun kammala, za su sanya kamfanin ya rika samar da metric tan miliyan 17 na sumunti. A cewarsa hakan zai sa kamafnin ya rage farashin sumunti zuwa naira 3,500 a kowane buhu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: