Masu Bahaya a waje a Birniwa zasu shiga tasku

0 214

Karamar Hukumar Birniwa ta haramta yin bahaya a bainar jama’a a garuruwa da kauyukan dake yankin karamar hukumar.

Shugaban Karamar Hukumar Muhammad Jaji Dole ya sanar da hakan a lokacin ganawa da manema labarai a Birniwa.

Ya hori magidanta da su gina shadda a gidajensu inda yayi gargadin cewar Karamar Hukumar ba zata laminci yin bahaya a bainar jama’a ba.

Jaji Dole ya yi alkawarin cewar Karamar Hukumar zata kiyaye da dokoki da kaidojin gwamnatin tarayya da ta jiha wajen ganin an fitar da karamar Hukumar daga cikin kananan hukumomi da ba a tsugunno a bainar jama’a a jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: