Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Shiyyar Kano (KEDCO) yace ya dauki matakan da suka kamata wajen kawo karshen korafe-korafen masu sabuwar mita da ake saka mata kati.
Jihoshin dake karkashin KEDCO sune Jigawa da Kano da Katsina.
Shugaban Sashen Yada Labarai na Kamfanin, Ibrahim Shawai, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.
- Barcelona ta ba Lamine Yamal lamba 10
- An ɗaura auren Umaru Musa Yar’Adua Jnr., ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Alhaji Umaru Musa Yar’Adua, tare da amaryarsa Maryam Ayuba Shuaibu
- Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar (GCON), ya kawo karshen shakku da tsokaci, inda a hukumance ya fice dga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),
- Manhajar TikTok ta goge fiye da bidiyo miliyan 3.6 a Najeriya saboda saba ka’idar dokokinta
- Tsohon Shugaban APC na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Edo, ya fice daga jam’iyya APC zuwa jam’iyyar hadaka ta ADC
Ibrahim Shawai ya sanar da cewa kamfanin ya dauki matakan inganta ayyukansa domin magance yawan korafe-korafe akan sabuwar mitar.
Yayi nuni da cewa an samu jan kafa wajen fara aiwatar da sabon kudin wuta kasancewar masu sabuwar mitar sun ki amincewa da katin wutar da suka saya farawa daga ranar 1 ga watan Satumba.
Yace kamfanin ya bayar da muhimmanci wajen magance korafe-korafen da suka shafi mita, domin biyan bukatar abokan hulda.