

Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya ta musanta rahotannin da ke zargin cewa mahara sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a shekaranjiya Litinin da rana.
Manajan Darakta na hukumar, Fidet Okiriya, wanda ya musanta hakan cikin wata sanarwa, yace rahotannin, kanzon kurege ne.
A cewarsa, akwai wasu bata gari wadanda suke yawan jefa manyan duwatsu kan jirgin kasa dake tafiya akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
- Goodluck Jonathan: Kuri’un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba
- Sarkin musulmi: Gobe Talata shine daya ga watan Ramadan
- Kamfanin Twitter zai kafa reshe a Afirka
- Kungiyar Barcelona ta fi ko wacce kungiya kudi a duniya
- Dalibai da yawa zasu rasa damar rubuta JAMB ta bana a Najeriya
Sai dai, ya bukaci masu amfani da jiragen kasan da kada su razana, kasancewar ministan sufuri da hukumar jiragen kasa zasu tabbatar da tsaron lafiyar yan Najeriya akan hanyar.
Kazalika, manajan sufurin jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna, Faskal Norli, ya tabbatar da cewa jirgin kasan ya isa tashar Idu a ranar Litinin kamar yadda aka tsara, kuma ya musanta duk wani hari daga mahara.