Matar Alhaji Aminu Dantata Ta Rasu

0 161

Matar hamshaƙin ɗan kasuwar nan na jihar Kano Alhaji Aminu Ɗantata, Hajiya Rabi Ɗantata ta rasu.
Hajiya Rabi Aminu Ɗantata wadda aka fi sani da Mama Rabi ta rasu ne a jiya Asabar a wani asibiti da ke birnin jidda na Saudiyya.
Mama Rabi ta rasu tana da shekaru 70 a duniya, bayan wata doguwar jinya da ta yi fama da ita.
Mama wadda ita ce mata ta biyu ga fitaccen ɗan kasuwar ta mutu ta bar ‘ya’ya shida ciki har da Tajudden Ɗantata da Batulu Dantata da Hafsa Dantata da Jamila Dantata sai kuma Aliya Dantata. Ta kuma mutu ta bar jikoki da dama.
Wani jikanta Sunusi Dantata ne ya tabbatar da mutuwar marigayiyar a shafin sa na tweeter.

Leave a Reply

%d bloggers like this: