Mutanen Yobe Zasu Yi Bikin Sallah A Takure Bayan Sanya Dokar Takaita Zirga-Zirga

0 202

Kwamishinan Yansandan Jihar Yobe, Abdulmaliki Sanmonu ya bayar da sanarwa takaita zirga-zirgan abeban hawa tsakanin gobe Asabar 10 ga watan Augusta da misalin karfe 11 na dare, zuwa ranar Lahadi, 11 ga watan Augusta, domin tabbatar da bukukuwan sallah babba cikin lumana.

Abdulmaliki Sanmonu ya fadi hakane cikin wata sanarwa da aka fitar a Damaturu jiya Alhamis, inda yace hakan wani mataki na tsare rayuka da dukiyoyi yayn bukukuwan.

Abdulmaliki Sanmonu ya nuna cewa takaitawar zata taimakawa jami’an tsaro wajen samar da ingattaccen tsaro tare da hana yan ta’adda katse bukukuwan.

Rundunar yansandan ta kuma tabbatarwa da jama’ar jihar wadataccen tsaro a guraren sallar idi da kuma guraren da ake taruwa kafin da lokacin da kuma bayan bukukuwan na Sallah Babba.

Kwamishinan sai kuma ya hori jama’a da su samar da bayanai masu amfani ga yansanda da sauran jami’an tsaro akan duk duk wata bakuwar fuska da abinda basu amince da shi ba. Sai kuma ya neme jama’a da suyi amfani da lokacin bukukuwan wajen gabatar da addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: