

- Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba - August 23, 2021
- Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da zasu fafata yaki da yan Taliban a Afghanistan - August 23, 2021
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara - August 23, 2021
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya yace rashin bayar da muhimmanci sosai ga bangaren ilimi shine ya haifar da matsalar tsaro dake addabar kasarnan.
Shugaban ya fadi hakane lokacin da ya karbi bakuncin tawagar mutanen jihar Adamawa, karkashin jagorancin Gwamna Ahmadu Fintiri, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Shugaban wanda ya dauki alkawarin duba bukatar tawagar, sai yace bangaren ilimi da na lafiya, sune suka fi muhimmanci a gwamnatinsa, musamman yadda gwamnatin tasa take kokarin samar da abeben more rayuwa da habaka arziki da dukkanin yan Najeriya.
Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman tattaunawar, Gwamna Ahmadu Fintiri yace sun je wajen shugaban kasarne domin yi masa bayani dangane da kalubalen da gine-gine da tituna suke ciki a jihar Adamawa.
Sagir kabir5050 says:
Allah yakyauta