Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta goyi bayan yajin aikin sai baba-ta-gani da ma’aikatan Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya, FCTA, suka tsunduma sakamakon rashin biyan albashi da bashin karin girma.
Yajin aikin da kungiyar JUAC ta shirya ya fara ne ranar Litinin a Abuja, inda ya kawo tsaiko a ayyukan ofisoshin FCTA da dama, yayin da ma’aikata ke zargin shugabanci da yin watsi da korafe-korafensu.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce bayan duba koken JUAC, an gano cewa ana kai wa ma’aikata hari kai tsaye ta hanyar kin biyansu hakkokinsu na halal.
NLC ta bayyana cewa rike albashin watanni biyar da bashin karin girma ba kuskuren aiki ba ne, illa zalunci ne da ya sabawa kundin tsarin mulki da ke kare hakkin ma’aikata.
Kungiyar ta kuma yi Allah-wadai da rashin tura kudaden fansho tun daga Mayun shekarar 2025, tana mai cewa hakan na barazana ga rayuwar ma’aikata da masu ritaya nan gaba.
Sai dai FCTA ta ce an samu ci gaba, inda ta bayyana cewa an magance bukatu 10 cikin 14, amma JUAC ta musanta hakan tana mai cewa babu wata yarjejeniya da aka aiwatar.
NLC ta umarci dukkan kungiyoyin kwadago a Abuja da su tsananta yajin aikin, tare da gargadin cewa ba za a janye ba har sai an cika dukkan bukatun ma’aikata.