Rayuka 21 Sun Salwanta Bayan Kwale-kwale ya Kife a Benue

0 62

Akalla mutane 21 ake fargabar sun mutu bayan wani jirgin ruwa ya kife cikin kogin Benue a Makurdi, babban birnin jihar Benue, jiya da rana.

A cewar wata majiya wacce ta shaida lamarin da idonta, wadanda hatsarin ya rutsa da su mambobin wata coci ce a garin Ijaha dake yankin karamar hukumar Makurdi, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa wani taro a tsallaken kogin.

Kakakin rundunar yansanda na jihar, DSP Catherine Anene, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa a madadin kwamishinan yansanda, Mukaddas Garba, yace an kaiwa yansanda rahoton aukuwar hatsarin a jiya da misalin karfe 2 da rabi na rana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: