Shugaba Bola Tinubu ya ce yana kokarin gyara tsarin hada-hadar kudi

0 223

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce yana kokarin gyara tsarin hada-hadar kudi da kuma tabbatar da tsarin kasafin kudi na gaskiya.

Shugaban ya bayyana haka ne jiya a Legas lokacin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya tarbe shi a gidan gwamnatin jihar da ke Marina.

A wajen taron akwai tsofaffin gwamnonin jihar da suka hada da Babatunde Fashola da Akinwunmi Ambode, da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki.

Tinubu ya yabawa Sanwo-Olu da ya karbi bakoncinsa tare da godewa sauran gwamnoni da manyan baki da suka zo karrama shi a wajen taron.

Ya kuma kara da cewa dole ne ya cire tallafin man fetur domin a dakile almundahana da kudin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: