Shugaban kasar Amukar Joe Biden da takwaransa na India Naranda Modi sun gana

Shugaban kasar Amukar Joe Biden da takwaransa na India Naranda Modi sun gana tare.
Sun gana ne jim kadan bayan yin jawabin a wurin taron tallafawa kananan kasashe, da ake gudanarwa a kasar Faransa.
Firaminitan Indiya, Narendra Modi ya nuna gamsuwarsa, kan alaƙar ƙasarsa da Amurka.
Narendra Modi ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi da ya gabatar wa haɗakar zaurukan majalisun ƙasar a birnin Washington DC.
Ya ce a yanzu ƙasashen biyu na son kyautata alaƙar haɗin gwiwa tsakaninsu.
Jami’an gwamnatin Amurkan sun yi ta yi masa tafi da jinjina yayin gabatar da jawabin, wani abu da ba a saba gani ba yayin da aka karɓi baƙuncin wani babban baƙo.
Shugaban na Indiyan, ya ce a yanzu zamanin zaman doya da manja tsakanin ƙasashen biyu ya zama tarihi, wani abu da ake kallo tamkar koma-baya ga ƙasar China.
Da yawa daga cikin mambobin jam’iyyar Democrat sun ƙaurace wa jawabin nasa, don nuna damuwa kan take hakƙin ɗan adam da suke zargin ana samu ƙarƙashin mulkinsa a kasar ta Indiya.