Tawagar Diflomasiyya Ta Saudiyya Ta Isa Birnin Tehran Na Kasar Iran

0 116

Ma’aikatar harkokin wajen Riyadh ta sanar da cewa, wata tawagar diflomasiyya ta Saudiyya ta isa birnin Tehran na kasar Iran domin tattauna batun sake bude ofisoshin diflomasiyyarta bayan shafe shekaru bakwai ba ta yi aiki ba.
Ziyarar ta biyo bayan ganawar da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka yi a kasar Sin cikin wannan mako bayan da suka amince a watan jiya na maido da huldar diflomasiyya.
Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyyar ta bayyana cewa, ziyarar ta ranar Asabar wani bangare ne na aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a ranar 10 ga watan Maris.
Ganawar da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka yi bayan masu zanga-zanga a Iran sun kai hari kan ofisoshin diflomasiyyar Saudiyya biyo bayan kisan da Riyadh ta yi wa wani fitaccen shugaban Shi’a.
Sarkin Saudiyya Salman ya gayyace shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi zuwa birnin Riyadh, ziyarar da aka shirya gudanarwa bayan watan Ramadhan mai alfarma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: