Zanga-Zanga Ta Barke A Yankin Amhara Na Kasar Habasha

0 109

Zanga-zanga ta ɓarke a yankin Amhara na ƙasar Habasha a rana ta biyar a jere kan nuna adawa da yunkurin gwamnati na soke dakaru na musamman a yankin.
Masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi ta hanyar saka duwatsu, inda suka yi ta ƙona tayoyi domin hana sojoji wuce wa.
Masu zanga-zangar na tsoron cewa matakin gwamnatin ƙasar zai janyo a riƙa kai musu hare-hare daga wajen makwaɓta.
Yawancin larduna a Habasha na da dakaru na musamman da ke kula da iyakokinsu da kuma faɗa da ƴan tawaye.
A makon da ya gabata ne, gwamnati ta sanar da cewa tana son haɗe dakarun na musamman zuwa sojojin tarayya ko kuma cikin ƴan sanda domin haɗin-kan kasa.
Matakin ya janyo gagarumar zanga-zanga a birane da kuma garuruwa da ke faɗin yankin.
Hakan kuma ya janyo saka dokar takaita zirga-zirga ta takaitaccen lokaci a birnin Gondar mai ɗimbin tarihi, inda aka ruwaito artabu tsakanin masu zanga-zanga da sojoji a garin Kobe, kusa da iyaƙa da yankin Tigray.
A ranar Lahadi ne firaministan Habasha, Abiy Ahmed ya sha alwashin zartas da matakin da ya ɗauka ko da hakan zai janyo wata matsala.

Leave a Reply

%d bloggers like this: