Tawagar ‘Yan Sanda Da INEC Zasuyi Bincike Da Kuma Gurfanar Da Hudu Ari

0 126

Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa Usman Alkali Baba ya umurci wata tawagar ‘yan sanda akan ta yi aiki tare da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC wajen bincike da kuma gurfanar da shugaban hukumar zabe na jihar Adamawa da aka dakatar Hudu Yunusa Ari.

A wata sanarwar da rundunar ta fitar wacce kakakinta Olumuyiwa Adejobi ya sanya wa hannu, babban sufeton ya ce ‘yan sanda za su tabbatar sun yi dukkan mai yiwuwa domin gano dalilin da ya sa Hudu ya aikata abun da ya yi.

Idan zamu iya tunawa dai, Ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa da aka ƙarasa, kwatsam Hudu wanda shi ne kwamishinan zaɓe na jihar, ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen.

Baba Alkali Usman ya ce a shirye suke su tabbatar an yi hukunci da ya dace kan dukkan wadanda aka samu da hannu a lamarin da ya faru a Adamawa domin martaba dokokin dimokradiya.

Sanarwar ta tabbatar wa ‘yan Najeriya da kuma kasashen duniya cewa ‘yan sanda za su binciki ayyana Aishatu Binani ta APC da Hudun ya yi tare sauran masu hannu a lamarin domin gurfanar da su a gaban kotu. Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin hukumar zaɓen ƙasar na dakatar da kwamishinan na INEC a Adamawa zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: