Za’a Yi Amfani Da Motoci Domin Kwaso Yan Najeriya Da Suka Makale A Sudan Maimakon Jirgin Sama

0 74

Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama ya ce ‘yan Najeriyar da suka makale a Sudan za a kwaso su zuwa nan gida Najeriya wajen amfani da motoci amaimakon jirgin sama.

Kafin hakan dai, mutane da dama ne suka makale a kasar da ke arewacin Afirka biyo bayan takaddamar wutar lantarki da ta haifar da rikici.

Amma da yake zantawa da manema labarai a jiya da yamma, Onyeama ya ce ba za a iya kwashe wadanda suka makale ta jirgin sama ba.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da wata sanarwa daga ofishin jakadancin Tarayyar Najeriya da ke birnin Khartoum, mai dauke da sa hannun H.Y Garko ta shawarci daliban da suka makale da su zauna a gida.

Gwamnatin Tarayya ta ce har yanzu yana da hadari a fara jigilar daliban zuwa kan iyakokin kasar Sudan ba tare da tabbacin tsaro daga hukumomin Sudan ba.

Har ila yau, Ofishin Jakadancin ya tabbatar wa daliban Nijeriya cewa, tsaron lafiyarsu shi ne abin da ya fi daukar hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: