A karon farko majalisar dokoki ta jihar Jigawa tayi bayanin ayyukan data gudanar a cikin shekara guda
A karon farko mjalisar dokoki ta jahar Jigawa tayi bayanin ayyukan data gudanar a cikin shekara guda.
Tun bayan rantsar da majalisa ta 8 a jahar Jigawa a ranar 14th Yuni, 2023, ayau kakakin majalisar Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin ya ƙira taron manema labarai inda yayi bayanin aikace-aikacen da suka gudanar a kafuwar majalisa ta 8 cikin shekara guda.
Cikin jawabin daya gabatar, kakakin majalisar ya bayyana cewa majalisar ta cika ƙa’idar zamanda ake buƙatar majalisa tayi a shekara inda sukayi zama har sau 184 wadda ya wuce adadin zaman da kudin tanadin doka ya bayar na zama sau 181 a shekara. Ya bayyana cewa hakan abin alfahari gareshi da sauran ƴan majalisu. Ya bayyana cewar cikin shekara guda majalisar ta aiwatar da dokoki guda 19 da kuma amincewa da wasu ƙudirori 27 dukkanin su masu muhimmanci ga cigaban al’ummar jahar Jigawa