Ambaliyar Ruwa A Yola Tayi Sanadiyyar Rasa Rayuka Da Asarar Dukiya Mai Yawa

0 110

Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 7 kawo yanzu, a wani iftila’in ambaliyar ruwa na ranar Alhamis a Birnin Yola.

Jami’in Hukumar mai kula da ayyukan hukumar a Jihoshin Adamawa da Taraba, Mista Abani Garki, shine ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Yola.

Ya lissafa wasu daga cikin guraren da ambaliyar ta shafa da Runde-Baru, da Wuro-Jabbe, da Damilu, da Yolde-Pate, da Bachure, da Kofare da kuma Jambutu, da sauransu. Dukkaninsu cikin Yankunan Kananan Hukumomin Yola ta Kudu da Yola ta Arewa.

Mista Abani Garki, ya alakanta yawan ambaliyar ruwa a dayawa daga cikin yankunan da abin ya shafa, da sakacin jama’a, inda yace mutane na shinge filayensu, suna sayarwa, ba tare da kyakykyawan tsarin gari ba.

Daga nan sai ya shawarci Gwamnatin Jihar Adamawa da ta duba matsalar filaye, sai kuma ya bukaci mutane da su gujewa gini a guraren da ke fama da ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: