An Tashi Rugagen Fulani Tare Da Kwace Gonakinsu, A Garin Chiroma Dake Jigawa Domin Samar Da Wajen Noman Rake

0 201

An tashi rugagen Fulani tare da kwace gonakinsu, a Garin Chiroma dake Karamar Hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa, domin samar da wajen noman rake, na kamfanin sukari mallakar mai arzikinnan dan Kasar China, Mr. Lee.

Jama’ar garin sunce ba gonakin Fulanin kadai aka kwace ba, mutanen garin Gayawan Mallam, wadanda shirin kamfanin ya shafa, sun rasa gonakinsu.

Wani daga cikin dattawan Fulanin, Mallam Hassan Haru, yace, lokacin da kamfanin yayi nufin fara aiki, sai aka basu kwanaki 3 su tashi daga wajen. Bayan kwanaki ukun sun kare, sai aka suka ga ‘yansanda dauke da makamai sun mamaye musu rugage, idan suka fitar dasu ta karfin tsiya.

Sai dai, wani daga cikin masu shari’a da suka kai kamfanin kara gaban kotu, Mohammed Rabi’u, yace duk da rigimar da ake yi, kamfanin ya cigaba da haka musu gonaki da sunan shimida fayip.

Yace hakan yasa masu gonakin baza su iya noma gonakinsu ba, kuma kasancewar rikicin yana gaban kotu a Gumel, hakan bai hana kamfanin cigaba da aikinsa ba.

Amma, sai yace suna sa rai, kasancewar kotun har ta fitar da dokar da ta bawa mutanen damar cigaba da noma gonakinsu, kafin a yanke hukunci.

Ya kuma kara da cewa, mafiya yawa cikin masu gonakin, ba a biyasu diyya ba, inda yace bayan lauyoyi sun gabatar da kwafin takardar biyan kudi, kusan mutane 7,000 basu karbi diyyarsu ba, amma an nuna cewa sun karba.

Da aka nemi jin ta bakin Daraktan Aikin Gona na Kamfanin, Umar Mohammed Majia, sai yace bazai yi magana ba, kasancewar rigimar na gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: