Babban Dalilin Da Yasa DSS Ta Gayyaci Magu Da Abinda Yasa Majalisa Taƙi Amincewa Da Shi A 2016

0 317

Hukumar DSS ta gayyaci shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu don ya amsa tambayoyi.

Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan da babban mai Shari’a na kasa Abubakar Malami ya zargi Hukumar EFCC da wasu rufe-rufa.

Babban mai ya nemi shuagaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsige Ibrahim Magu saboda manya-manyan zarge-zargen da ake yi masa ciki har da karkatar da wasu kuɗaɗen da aka kwato.
Bugu da kari Malami ya zargi Magu da karya ka’idar aiki gami da yin gaban kansa tare da rashin da’a.

Rahotani sun bayyana cewa Magu ya tafi zuwa Hadaddiyar daular Larabawa a lokacin da aka saka dokar kulle saboda Korona ba tare da sahalewar shugaban kasar Muhammadu Buhari ba.

Bayan da aka tambaye shi sai ya ce ya je wani bincike ne.

Haka kuma na zargin kudaden da yake kashewa da yadda yake tafiyar da rayuwarsa bai kai ga samun da matsayin sa ba.

Koda a shekarar 2016 sai da Majalisar kasa ta ki amincewa da tattbatar da shi a matsayin shugaban hukumar ta EFCC saboda wani rahoton sirri da hukuma DSS ta bayyana cewa yana da kashi a gindinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: