Gwamnatin Jigawa ta kashe Naira miliyan 500 wajen gina ingantattun bandakai a fadin jihar

0 370

Gwamnatin Jigawa ta ce ta kashe naira miliyan 500 wajen gina ingantattun bandakai a makarantu da asibitoci da kasuwanni da wuraren taruwar jama’a a fadin jiha.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Alhaji Ibrahim Hannun Giwa, wanda ya bayyana haka a Dutse, ya ce gwamnati ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da dorewar matsayinta na Jihar data yi bankwana da bahaya a bainar jama’a.

A cewar Hannun Giwa, jihar Jigawa na shirin magance yin bahaya a bainar jama’a nan da shekarar 2025.

Hannun Giwa ya ce an samu nasarar hakan ne ta hanyar aiwatar da manufofi da shirye-shirye masu inganci tare da hadin gwiwar ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF. Kwamishinan ya kara da cewa jihar ta kafa wani kwamiti da zai tsara hanyoyin da za’a bi domin dorewar matsayin ta na wacce tayi bankwana da barazanar bahaya a bainar jama’a gaba daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: