Gwamnatin Tarayya na iya waiwaitar Majalisar kasa domin yin duba kan kasafin kudin 2024

0 132

Ministan Kudi, Wale Edun, ya ce Gwamnatin Tarayya na iya waiwaitar Majalisar kasa domin kara duba kan karin kudaden shiga a kasafin kudin 2024 idan kasar ta samu ingantaccen tsarin kudaden shiga a shekara mai zuwa.

Ministan ya bayyana haka ne jiya a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudin ma’aikatar sa.

Edun ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta dogara ne da tanadi don bunkasa samar da kudade don gudanar da kasafin kudin 2024, tare da nuna cewa Gwamnatin Tarayya na iya yin la’akari da karin kasafin kudin.

Majalisar dattijai ta bukaci ministan kudin da ya yi kokarin kawar da matsalolin da ke tattare da jinkiri wajen aiwatar da kasafin kudin idan ya samu amincewa.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa, Sani Musa, ya kuma bayyana damuwarsa kan gazawar gwamnati wajen gaggauta aiwatar da karin kasafin kudin shekarar 2023. A ranar 29 ga Nuwamba ne, 2023, Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da kididdigar kasafin kudin sa na farko na kimanin Naira tiriyan 27 na shekara 2024 ga zauren Majalisar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: