Kimanin mutane 11 ne suke bukatar Agaji a Najeriya

0 99

Shugaban Hukumar Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Mista Mr Edward Kallon, ya ce kimanin mutane 11 ne suke bukatar Agaji a Najeriya.

Mista Edward Kallon, ya bayyana cewa rahoton ta’addanci a Duniya na shekarar 2020, ya yi nuni da cewa Najeriya ce ta uku cikin jerin kasashen da suke fama da ta’addanci a Duniya, bayan Afghanistan da Iraq.

Jami’in ya bayyana hakan ne a birnin Makurdi a lokacin da yake yiwa Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom bankwana, biyo bayan karewar wa’adinsa kimanin shekaru 5 kenan.

A cewarsa, rikicin Fulani da Manoma a yankin Arewa ta tsakiya, da hare-haren yan Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas da hare-haren yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma da kuma hare-haren yan Biafra da tsagerun Neja Delta na daya daga cikin dalilan da suka sanya aka samu yawan yan gudun hijira.

Haka kuma ya ce yana farin ciki bisa yadda kasashen Duniya suka san halin da Jihar Benue da Najeriya suke ciki.

Da yake bayar da Jawabi, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom, ya ce ya yi farin ciki da aka gabatarwa  Majalisar dinkin Duniya rahoto abinda yake faruwa a Najeriya, inda ya bukaci a gabatar da irin wannan rahoto ga fadar shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: