MDD ta ware $15m domin yaki da Ebola a Guinea da Congo

0 90

Majalisar Dinkin Duniya ta ware kudi dala miliyan 15, kwatankwacin naira miliyan dubu 5 da miliyan 800, domin yakar sabbin barkewar annobar Ebola a kasashen Guinea da Jamhuriar Demokradiyyar Kongo.

Jagoran agaji na majalisar dinkin duniya, Marka Lowcook, wanda ya sanar da haka a jiya, yace wannan shine kashin farko na kudaden da majalisar dinkin duniya zata fitar.

Da yake yiwa manema labarai jawabi, kakakin majalisar dinkin duniya, ya rawaito Lowcook na cewa kudaden zasu taimakawa kasashen Guinea da Jamhuriar Demokradiyyar Kongo su kula da barkewar cutar tare da tallafawa shirye-shiryen kasashe makota.

Kasar Guinea ta ayyana sabuwar barkewar cutar Ebola a ranar 14 ga watan Fabrairu, shekaru 4 bayan barkewar cutar Ebola mafi muni a Afirka ta Yamma, tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016. Wannan barkewar tayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 11 da 300, mafiyawa yawansu a kasashen Guinea da Saliyo da Liberia.

Leave a Reply

%d bloggers like this: