Majalisar zaratarwa zata sayo taki domin wadanda rikici da ambaliyar ruwa ya shafa

0 134

Majalisar zartarwa ta tarayya a jiya ta amince da naira Miliyan 922 da Dubu 800 domin sayen takin zamani da nufin taimakawa jihoshin da rikici ya shafa da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2018.

Ministar jin kai, annoba da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron majalisar.

Ta ce jihoshin da za su ci gajiyar shirin, wadanda suka hada da Adamawa, Borno da kuma Yobe, za su samu nau’ikan takin zamani na NPK a matsayin tallafi ga manoma.

Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman, ya ce majalisar ta amince da wasu abubuwa biyu daga ma’aikatar sa. Ya ce, amincewar ta hada da sayo taransfoma guda hudu akan kudi Naira Biliyan 3 da Miliyan 200 domin inganta ingancin samar da wutar lantarki a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: