

Mutane goma sha shida aka bayar da rahoton sun mutu, yayin da daruruwan gidaje da gonaki suka salwanta a ambaliyar ruwa daban-daban da aka samu a yankunan kananan hukumomi bakwai na jihar Jigawa.
Sakataren zartarwa na hukumar agajin gaggawa ta jiha, Yusuf Sani Babura, ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse.
Yace an samu ambaliyar ruwan sanadiyyar mamakon ruwan sama cikin makon da ya gabata.

Kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Taura, da Jahun, da Babura, da Ringim, da Dutse, da Birnin-Kudu, da Miga, da Kafin-Hausa, da Auyo, da Gwaram, da Malam-Madori, da Birniwa da kuma Kaugama.
- Tarihin Gamuwa 10 Tsakanin Kano Pillars VS Eyimba Da Kuma Wasan Yau
- Abubuwa 5 da suka zama wajibi lokacin sanyi
- An ƙaddamar da kudin kariya ga ƴan jarida da masu fafutukar ƴancin amfani da yanar gizo
- Yadda ake duba suna don zama ma’aikacin damara na 2020 a Nijeria
- Me Ƙungiyar Izala ta ce kan matsalolin tsaro a Najeriya?
Sani Babura yayi bayanin cewa mutane sun mutu yayin da gine-gine suka zube a lokacin da ake ruwan sama, kuma mutane da dama sun samu raunuka daban-daban.
Ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta kuma yi awon gaba da dubban gonaki, inda ta lalata amfanin gona.