Za a fito da sabbin hanyoyin tafiyar da manyan makarantu a Jigawa – Lawan Yunusa Danzomo

0 103

Kwamishinan ilimi, Kimiyya da fasaha na jihar Jigawa, Dakta Lawan Yunusa Danzomo ya bukaci kwalejojin fasaha su bujuro da tsare-tsare na bai-daya domin tafikar da al’amuransu yadda ya kamata.

Kwamishinan ya yi wannan kiran ne lokacin kaddamar da kwamitin da zai tsara ka’idojin aikin ma’aikatan kwalejojin fasaha wanda aka gudanar a kwalejin fasaha ta jiha dake Dutse.

Dr. Lawan Yunusa Danzomo

Wakilan kwamitin sun hadar da magarakardar kwalejin fasaha ta jiha dake Dutse da na kwalejin Binyaminu Usman dake Hadejia da na cibiyar fasahar sadarwa ta jiha dake Kazaure da kuma wasu ma’aikatan kwalejojin.

Yace an dorawa kwamitin alhakin yin kyakykyawan nazari kan dokokin aikin gwamnati tare da sauran dokokin da suka tanadi aiwatar da harkokin kwalejojin.

A jawabin da ya gabatar amadadin wakilan kwamitin magatakardar cibiyar fasahar sadarwa ta jiha dake Kazaure, Malam Sadisu Buhari ya godewa m’`aikatar bisa basu damar gudanar da wannan aikin, inda ya yi alkawarin zasu gudanar da aikin kamar yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: