Kimanin mutane 23 ne suka rasa rayukansu a sakamakon illar da ambaliyar ruwa ta haifar a jihar Jigawa wanda yayi sanadiyyar raba mutane dubu 51 da muhallinsu a kananan hukumomi sama da 24 a nan jihar.
Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa SEMA Yusuf Babura shine ya tabbatar da mutuwar mutane 21 a jiya, wanda yace mafiya yawa kananan yara ne.
Babura yace dayawa daga cikin wanda ambaliyar ruwan ta shafa sun rasa rayukansu a sakamakon rushewar gini wanda mamakon ruwan sama ya haifar a yankunan, sai sauran da igiyar ruwa ta hallaka.
Haka kuma yace sama da iyalai dubu 50 sun kauracewa muhallinsu na gado, a yayinda akayi asarar dubban kadadan filayen noma tare da tare da rasa kayan amfanin noma.
Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da kauyukan Maruta, Babaldu, Samamiya duka a kananan hukumomin Birnin Kudu da Gwaram. Kayan amfanin gonar da akayi asara kuwa suna kamar haka Yabanyar Dawa, Masara, Shinkafa, da Gero, wanda kudin yakai kimanin biliyoyin Nairori.
- Ronaldo ya yi alfahari da ɗansa ya buga wa Portugal tamaula
- Gwamna Uba Sani Ya Kafa Sabon Tarihi, Ya Yi Abin da ba a Taba Yi ba a Najeriya
- Tsohun gwamnan jihar Benue,ya baiyana cewa jam’iyyar PDP tana cikin mawuyacin hali da zai iya kai ta ga rushewa kafin 2027
- Sojoji masu mulkin Mali sun rusa dukkan jam’iyyun siyasa a kasar
- NiMET, ta fitar da sabon hasashen yanayi inda tace da yiwuwar ɓarkewar cututtukan ruwa a karshe shekara 2025
Kazalika aftilain ya shafi kananan kukumomi 24 daga cikin kananan kumomi 27 na jihar, wanda kuma abin yafi Kamari a kananan hukumomi 17. Babura yace kawo yanzu, hukumar bada agajin ta dunguma shirin raba kayan tallafi ga alumar da iftilain ya shafa, wanda dayawa daga cikin su suka yi hijira zuwa makarantu da zama