Ofishin hukumar wayar da kan jama`a ta kasa a jihar Jigawa ta gudanar da taron gangami a karamar hukumar Malam-Madori domin fadakar da al`umma illolin da cutar Korona virus ta haifar a fannonin tsaro da zamantakewa.
A jawabin da ya gabatar Daraktan hukumar na jiha, Malam Shu`aibu Karamba Haruna yayi dogon bayani akan matakan da ya kamata a dauka domin kare yaduwar cutar Covid-19.
- NEMA ta tarbi ƴan Najeriya 147 da aka dawo da su daga Nijar
- Najeriya za ta kwashe mutanenta daga Isra’ila da Iran
- INEC ta yi watsi da sanarwar taron NEC na Jam’iyyar PDP
- Gwamnatin Jigawa ta ware naira biliyan 2 domin gina magudanan Ruwa da Gadaje
- Najeriya ta shigo da danyen man fetur na sama da naira tiriliyan 1.19 a cikin watanni uku
Haka kuma ya bukaci jama`a su tabbatar suna bin dukkanin ka`idojin da hukumomin lafiya suka tanada domin kare yaduwar cutar.
A lokacin gangamin wani jami`in hukumar wayar da kan jama`a ta kasa, Malam Tijjani ya gabatar da makala mai taken tasirin cutar Covid-19 akan tattalin arziki da karuwar aikata laifuka da kuma rigingimu tsakanin Fulani da manoma.
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Malam-Madori wanda ya sami wakilcin Daraktan tsare-tsare na yankin, Malam Lawan Bawa ya jaddada kudurin karamar hukumar na hada kai da hukumar domin cimma biyan bukata.
Mahalarta taron sun hadar da yan`kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyar Miyetti Allah da jami`an hukumar kiyaye haddura ta kada limamai da masu ruwa da tsaki.