Daga yanzu gwamnatin Jihar Jigawa ce zata ke ɗaukar ɗawainiyar jami’ar Jiha dake Kafin Hausa.

A cikin makon nan ne dai kora ta turnuke gajimare kan batun wani kudiri da ake ganin zai gurgunta jami’ar, kudirin kuwa shi ne wanda zai janye wajibcin biyan kashi 2% na abinda kowacce ƙaramar hukuma ta samu a rabon tattalin arziki.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar A yayin jawabi yau a babban birnin Jiha dake Dutse, ya ce dokar da ta tilastawa biyan kashi 2% ta zama kamar karfe ƙafa ce domin a halin da ake ciki wasu ƙananan hukumomin albashi ma da kyar suke iya biya.

Saboda da haka ne ya ce hakki ne na kowacce gwamnatin jiha ta ɗauki nauyin jami’ar Jiharta ba na ƙananan hukumomi ba.

Tun farko dai a cewar Gwamnan sun taras an bayar da kwangilar ginin jami’ar ne kan kuɗi Naira Biliyan 7 amma gwamnatin da ta gabata ta iya biyan Naira N3b ne kacal.

Bayan zuwan gwamnatinsa suka ci gaba da biya har kawo yanzu sun kashe sama da Naira biliyan 5b a makarantar.

Wannan sanarwa da gwamnan ya bayar na nufin kenan jiha ta karbe ragamar tallafi da ɗawainiyar gudanar da jami’ar daga tsohuwar dokar da ta kallafawa kananan hukumomi yake na kashi 2% na kuɗaɗensu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: