NEMA ta shirya domin raba kayayyakin abinci wanda hakumar jin kai da kasar saudiyya ta samar

0 97

Hakumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta shirya domin raba kayayyakin abinci wanda hakumar jin kai da kasar saudiyya ta samar, inda ake sa ran gidauniyar tallafin jin kai da bayar da agajin gaggawa ta King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre (KSrelief) zata tallafawa mutane dubu 5,606.

Masu cin gajiyar wanda sun kasance daga jihohin Kano, Jigawa, da jihar Katsina da kuma makarantun Tsangaya a Maiduguri babban Birnin jihar Borno.

Kakakin hakumar ta NEMA Ezekiel Manzo yace kayayyakin da za’a raba sun hada da buhun shinkafa mai nauyin kilo giram 25, da buhun wake mai nuyin kilo 25, da kilo 4 na garin masa vita, lita 2 na mai, da kilo 2 na tumatir, da kilo 1 na gishiri da kuma maggi. Jumillar magidanta dubu 5,606 zasu amfana da rabon ana sa ran zasu rabauta da kilo 59 na kayyakin abincin. Hakumar NEME da hakumomin bayar da agajin gaggawa na jihohi SEMA ne zasu zabo masu cin gajiyar kayayyakin abincin a jihohin Kano, Jigawa da jihar Katsina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: