Sabbin Bayanai Kan Halin da Ake Ciki A Jigawa Kan Cutar Korona

0 244

1- Bayan Fitowar sabbin bayanai Jihar Jigawa yanzu na da masu ɗauke da Korona 9

2- Mutum na farko a jihar ya rasu a dalilin cutar

3- Kwamishinan Lafiya kuma shuganan kwamitin ko ta kwana kan yaki da cutar na Jihar Dr Abba Zakari ne ya sanar da hakan a babban birnin jihar Dutse, a wani taron manema Labarai jiya

4- Sabbin ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗar da; 

Dutse

Gwaram

Miga

Auyo

Birnin Kudu

Gumel

Gujungu a ƙaramar hukumar Taura

Duk za a kulle ranar Juma’a da karfe 12:00am (Dare) Kazaure na cikin lissafi

5- Gwajin waɗanda ake zargin na da cutar har yanzu babban kalubale ne a jihar Jigawa saboda babu wurin gwaji sai an je Kano ko Abuja, amma ana duba yiwuwar fara tuntubar asibitoci masu zaman kansu da hukumar NCDC ta tantance

6-Kamishinan lafiyar ya ce gwamnatin Jigawa zata fara rabon kayan abinci don rage raɗaɗin halin da ake ciki

7- Sai dai an samu bambancin lissafi idan aka kwatanta da alƙaluman da hukumar NCDC ta bayyana na masu ɗauke da cutar, hukumar a daren jiya ta ce, tana da labarin mutane 7 ne kacal dake da cutar a Jigawa sabanin 19 da gwamnatin jihar ta sanar (Duba cikin hoton ƙasan labarin)

Leave a Reply

%d bloggers like this: