Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin magance matsalar shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi

0 327

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana kokarin gwamnatin sa na magance matsalar shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi a Nigeriya.

Shugaban kasar ya bayyana haka a fadar shugaban kasa yayin wani taro da aka shirya na ranar yaki da ta’ammali da kuma safarar miyagun kwayoyi na duniya.

Shugaba Tinubu,yayi alkawarin magance matsalar shaye-shaye, inda yayi kira ga gwamnatoci,kungiyoyin kasashe da masu ruwa da tsaki da su dauki matakin da ya dace wajen kare al’umma daga illar amfani da miyagun kwayoyi.

Kazalika, ya bukaci shugabannin addinai, na gargajiya, cibiyoyin ilimi,da shugabannin kungiyoyin fararen hula da sauran yan kasa da su hada kai da gwamnatin wajen magance matsalar shaye-shaye. Anasa jawabin,shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Birgediya Janar Buba Marwa mai ritiya, ya ce hukumar ita kadai baza ta  iya magance matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi ba sai an samu hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: