Rundunar yansandan jihar Jigawa ta kame mutane 20 da take zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da kisan kai, inda ta kwato kayan sata daga hannunsu da kuma makamai.
Kwamishinan yansanda na jiha, Usman Sule Gomna, ya sanar da haka a taron manema labarai a Dutse.
Kwamishinan ya bayyana cewa tawagar yansanda ta musamman masu yaki da fashi da makami sun kai farmaki kan wasu maboyar ‘yan fashi a yankin karamar hukumar Ringim inda suka damke wasu daga cikin ‘yan fashin.
- Gwamnatin jihar Anambra ta haramta raba
- Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da daukar sabbin jami ai 130, 000 da zasu kare dazukan Nijeria
- Najeriya ba za ta koma mulkin soja ba – Yakubu Gowon
- Kotu ta yankewa tsohon shugaban Maurtania wa’adin zaman gidan kaso
- Ƙungiyoyin malaman makarantu sun shiga yajin aiki a Nijar
Ya kara da cewa jami’an yansanda a karamar hukumar Babura sunyi arangama da wasu yan bindiga 9 a kauyen Andau dake yankin karamar hukumar.
Sule Gomna ya kuma ce tawagar yansanda ta musamman masu yaki da fashi da makami sun kama mutane 10 da ake zargin barayine yan bindiga a kwaryar birnin Dutse.