Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwa bisa karuwar cin zarafin mata, musamman fyade a jihar, inda yayi alkawarin sanya dandaka a cikin sabuwar dokar cin zarafin bil’adama wacce ya sanyawa hannu kwanannan.
Bala Mohammed ya fadi haka lokacin da ya karbi bakuncin ministar harkokin mata da cigaban yara, Pauline Tallen, wacce ta kai masa ziyarar aiki jiya a gidan gwamnati dake Bauchi.
- Amina Mohammed Ta Buƙaci A Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Al’umma, Ta Ce Makomar Afirka Na Hannun Matasa
- Tinubu Ya Amince da Ware Naira Biliyan 45 Domin Sa Ido Kan Cututtuka A Filayen Jiragen Sama Biyar
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Aiwatar da Yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya Ta Kulla Ta 2025 A SLUK
- Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Kawo Karshen Matsalar Tsaro — Bafarawa
- “Zan Iya Sadaukar da Raina Domin Tinubu” — Uba Sani
Gwamnan yace za a mayar da dokar cin zarafin bil’adama zuwa majalisar dokokin jihar, domin tabbatar da an gyare-gyare a inda aka samu sabani.
Tunda farko, a jawabinta, ministar harkokin mata da cigaban yara, Pauline Tallen, ta bayyana fyade a matsayin abinda yafi kisan kai muni.
Comments are closed.